Daga Hussaini Ibrahim, Gusau Kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar Zamfara, ta gudanar da taron addu'a domin samun nasara akan yakin...
Daga Hussaini
Ibrahim, Gusau
Kungiyar Kwadago ta kasa reshen jihar
Zamfara, ta gudanar da taron addu'a domin samun nasara akan yakin da Gwamnati
ke yi da ‘yan Bindiga da suka addabi al'ummar Jihar Zamfara.
Shugaban Kungiyar na Jihar Zamfara, Kwamared Sani Halliru ne ya jagoranci gabatar da
addu'ar a hedikwatar kungiyar da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Kwamared Sani Halliru ya bayyana
cewa, ‘yan Bindigar sun gurgunta ayyuka a ma'aikatun jihar ta Zamfara sakamakon
dauki dai dai da suke yi wa ma'aikatan domin neman kudin fansa, inji Kwamared
Sani Halliru.
Kuma ya kara da cewa, yanzu haka a
cikin satin nan ‘yan Bindigan sun yi awon gaba da Shugaban Ma"aikatan
gwamnati, Kwamared Sidi Ibrahim a gidansa da ke Karamar hukumar Bukkuyum bayan
sun sako Daraktan lafiya da wasu Ma'aikatan da aka biya kudin fansa; “akan haka
muka shirya wannan addu'ar na ganin kudirin gwamna Matawalle da jami'an tsaro
ya cika na ganin an gama da 'yan Bindiga da suka addabi Jihar Zamfara”, inji
shi.
A nasa jawabin Mai Martaba Sarkin
Katsinan Gusau, Alhaji Ibrahim Bello ya bayyana cewa, rashin taimakon 'yan’uwa
ga masu hali ne da rashin zumunci ya kara jawo yin garkuwa da mutane; “domin za
ka ga a gida Allah ya yi wa karami arziki bai iya taimakon Yayan sai ya bar shi
ya kwana da yunwa, wannan ya sanya wasu shiga cikin gungun miyagu. Sada zumunci
kuwa a nan ne mutum zai ga wanda zai taimaka a cikin danginsu idan ya ziyarce
su ya ga halin da suke ciki”, inji Mai Martaba Sarkin Katsinan Gusau.
Kuma ya yi kira da babbar murya akan
taimakon mabukata da sada zumunci, da kuma yin addu'a da sadaka domin sune ke
kare masifa a cewarsa.
A nasa jawabin Shugaban Ma'aikatan
Jihar Zamfara, da ya samu wakilcin Babban Sakataren a ofishinsa, Alhaji Yusuf
Bakura , ya nuna jindadinsa ganin yadda kungiyar Kwadago ta damu da halin da
al'umma ke ciki har ta shirya addu'a domin samun nasara akan ‘yan Bindiga da
suka addabe mu.
No comments