Kwana Guda Da Harba Makami Mai Cin Nisan Zango Amurka Ta Nemi Sulhu Da Koriya Ta Arewa

 


Wakilin shugaba Biden a Koriya ta Arewa ya ce kofa a bude ta ke domin tattaunawa, kwana guda bayan kasar ta yi nasarar gwajin makami mai linzami mai cin dogon zango.

Sung Kim na magana ne a wani taro da aka yi a birnin Tokyo na Japan, tare da manyan jami'an gwamnatin Japan da kuma Koriya ta Kudu.

Mista Kim ya ce ya na son bayyanawa karara cewa Amurka ba ta da niyyar tsaurarawa Koriya ta Arewa.

Wakilai uku na tattaunawa kan hanyar da za su karfafawa Pyongyang gwiwar komawa teburin sulhu, ana kuma sa ran za su yi wa Arewar tayin kayan agaji a daidai lokacin da ta ke fama da matsin tattalin arziki da karancin abinci.

-BBC Hausa


Post a Comment

0 Comments