A yau Alhamis 16 ga watan Satumban 2021 ne aka dawo kotun dake gidan Sarki Kofar Kudu domin ci gaba da saurarar Shari'ar Sheikh Abdu...
A
yau Alhamis 16 ga watan Satumban 2021 ne aka dawo kotun dake gidan Sarki Kofar
Kudu domin ci gaba da saurarar Shari'ar Sheikh Abduljabbar Kabara, sai dai a
yau lauyoyinsa ba su zo ba, sai mutum daya daga cikin su, Barista Haruna
Magashi wanda ya sanar da janyewa daga wakiltar Abduljabbar Kabara a kotun
kamar yadda majiyarmu ta Jarida Radio ta tabbatar mana.
Jarida
Radio ta labarto cewa; a baya kotun ta bada umarnin duba lafiyar kunnen
Abduljabbar da kuma kwakwalwarsa, kuma an zo da sakamakon asibitin Murtala inda
suka tabbatar da cewa kunnen Abduljabbar lafiya kalau yake.
Sannan
rahoton asibitin Dawanau shima ya tabbatar da cewa Abduljabbar lafiyarsa kalau.
Sai dai an taba bashi gado a asibiti ƙwaƙwalwa sanda suka taba fada da Dan
uwansa ya yi kwana hudu asibitin amma a wannna lokacin ba a yi masa gwajin
kwakwalwa ba, kuma ba a dora shi akan wani magani ba.
Dan
uwansa Kasiyuni na daga waÉ—anda suka raka shi gwajin, kuma ya ce haka ba wani
abu bane race jazaba ta mabiya darikar sufaye da akan samu da yawa daga cikin
mabiya Sufanci da yin haka.
A
halin yanzu Alkali Ibrahim Sarki Yola zai fadi matsayarsa kan bukatar lauyoyin
na janyewar daga ƙarar.
Bayan
saurarar rokon Lauyoyin Abduljabbar na janyewa daga kare shi, Alkali Sarki Yola
ya tambayi Abduljabbar kan janyewar lauyoyin nasa:
Malam
Abduljabbar Nasir Kabara ya ce a cikin tambayoyin da ya yi ma Lauyoyinsa suka
kasa ba shi amsa, shi ne na yi kan hana shi magana a zaman kotun da ya gabata lokacin
aka karanto masa sabbin tuhuma.
Lauyoyin
Abduljabbar sun yi suka kan maganarsa, sannan suka nemi da a amince da
bukatarsu na janyewa.
Alkalin
ya amince da bukatar janyewar Lauyoyin Abduljabbar na janyewa daga kare
Abduljabbar a shari’ar.
No comments