Majalisar dokokin jihar Legas ta rattaba hannu kan dokar hana kiwo a cikin jama’a. Majalisar dokokin jihar Legas da ke kudancin Nijeriya t...
Majalisar dokokin jihar Legas ta rattaba hannu kan dokar hana kiwo a cikin jama’a. Majalisar dokokin jihar Legas da ke kudancin Nijeriya ta amince da dokar hana kiwo a cikin jama'a a dukkan sassan jihar a zamanta na jiya Alhamis.
Tun a jiya ne Kakakin majalisar Mudashiru Obase ya bukaci a miƙa wa gwamnan jihar Babajide Sanwo-Olu kwafin amincewar nan take.
Jihohi da dama a kudancin Nijeriya na ci gaba da amincewa da dokar hana kiwo a cikin jama'a da zummar magance matsalar tsaron da suke fuskanta.
Yawanci mutane na danganta hare-haren da ake ka iwa yankin da makiyaya, sai dai sun sha musanta cewa suna da hannu.
No comments