Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Maryam Abacha American University dake Jamhuriyyar kasar Nijer, ta sauke tutocinta kasa-kasa domin makokin ra...
Hukumar gudanarwa ta Jami’ar Maryam
Abacha American University dake Jamhuriyyar kasar Nijer, ta sauke tutocinta
kasa-kasa domin makokin rasuwar Muhseen
Bala muhammad Tukur wanda Allah ya yi wa rasuwa sakamakon rashin lafiya a ranar
Alhamis din 16 ga watan Satumban 2021a Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano.
Marigayi Muhseen Bala Muhammad daya
ne daga cikin daliban Jami’ar ta MAAUN wanda
ke karatun ilimin sanin kwamfuta da fasahar bayanai (Computer Information
Technology) a matakin aji biyu (200 level).
![]() |
Marigayi Muhseen Bala |
Sakon ta’aziyyar na dauke ne da sa
hannun shugaba kuma Mu’assasin Jami’ar Maryam Abacha American University da
Franco-British International University dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar
Gwarzo, wanda aka raba wa manema labarai kwafinta a Kano a yau Juma’a 17 ga watan Satumban 2021.
Hukumar gudanarwa ta Jami’ar ta
bayyana rasuwar dalibin a matsayin babban rashi ba kawai ga iyayensa da
‘yan’uwansa ba, ga kafatanin ma’aikatan makarantar.
Shugaban MAAUN har wala yau ya
bayyana Marigayin a matsayin dalibi mai ladabi wanda yake girmama Dattawa,
musamman Malamansa.
Farfesa Abubakar Gwarzo ya ce
"A madadin Hukumar Gudanarwar ta Jami'ar Maryam Abacha American University
ta Nijer, ina mika sakon ta'aziyya ga iyaye, 'yan’uwa da abokan musamman
mahaifinsa wanda shi ne Daraktan kulla Alaka na Jami’ar, Dr Bala Muhammad Tukur
da mahaifiyarsa bisa rasuwarsa", Inji Farfesa Abubakar Gwarzo.
A
karshe ya yi addu’ar Allah madaukakin Sarki ya sanya Marigayin a Aljannah
Firdaus ya kuma bai wa iyalansa jure wannan rashi mai radadi.
No comments