Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

MAAUN Ta Taya Adamu Muhammad Murnar Cika Shekaru 36

Shugaba kuma wanda ya kafa Jami'ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University dake Kaduna,...Shugaba kuma wanda ya kafa Jami'ar Maryam Abacha American University da Franco-British International University dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya taya Alhaji Muhammad Adamu Wakili murnar cikarsa shekaru 36 a duniya a ranar Lahadi 19 ga watan Satumba. 


Sakon taya murnar na dauke ne a cikin takardar da Farfesa Abubakar Gwarzo ya sanyawa hannu kuma aka aikawa Muhammad Adamu Wakili, Rajistarar Jami'ar Maryam Abacha American University dake kasar Togo.
 

Farfesa Abubakar Gwarzo wanda har wala yau shi ne shugaban kungiyar Jami'o'i masu zaman kansu, ya bayyana Wakili a matsayin mutum mai gaskiya da amana wanda yake huldar mutunci da al'umma tare da jajircewa wajen ganin matasa musamman a Arewacin Nijeriya da Nijeriya baki daya sun samu nagartaccen ilimi.  

Ya kuma bayyana Adamu Wakili a matsayin abin koyi ga matasa wadanda ke girmama Dattawa da ma kananan yara wanda hakan babban nasara ce gare shi damu baki daya. 

"Bisa wannan, a madadin Hukumar gudanarwa ta Maryam Abacha American University da Franco-British International University, ina taya ka murnar cika shekaru 36", inji Farfesa Gwarzo. 

"Allah madaukakin Sarki ya ci gaba da yi wa rayuwarka albarka, ya kuma baka kwarin guiwar ci gaba da jagoranci abin misali," inji Farfesa Abubakar Gwarzo. 

Wanda ake taya murna, Adamu Muhammad Wakili mashawarcin ilimi ne, masanin harkokin al'umma, mai kawo sauyi ne, kuma mai sharhi kan harkokin siyasa. 

Har wala yau ya yi aiki da Jami'ar ESAE dake kasar Benin, a matsayin jami'in bada shaidar shiga Jami'ar, daga bisani ya zama Sakataren Ilimin kafin ya zamo Rajistara duk a Jami'ar. 

No comments