Daga Ammar M. Rajab Da yake zantawa da gidan Talabijin na PRESS TV dake Iran da yammacin ranar Larabar 29 ga watan Satumban 2021, a hirars...
Daga Ammar M. Rajab
Da yake zantawa da gidan Talabijin na PRESS TV dake Iran da yammacin ranar Larabar 29 ga watan Satumban 2021, a hirarsa ta farko da wata kafar watsa labarai tun bayan sakinsa da aka yi daga tsarewar da aka yi masa da shi da matarsa Zeenat Ibrahim na kusan shekaru shida, Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky ya ce yana da tabbaci cewa mafi yawan al’ummar Nijeriya za su fi zabar tsarin Musulunci idan abin a ba su zabi ne.
"Na yi imanin cewa idan za a yi wani taro a ƙasar nan kuma za a tambayi mutane 'wane tsarin kuke so? Shin halin da ake ciki (kuke so) wanda aka gada daga turawan mulkin mallaka na Biritaniya ko tsarin musulunci? Na tabbata mafi yawan mutane za su zabi tsarin Musulunci. [Domin] za ta zama gwamnatin mutane ne bayan komai, ”in ji shi.
Shaikh Zakzaky ya ce, duk da cewa, hukumomi a Nijeriya sun hana irin wannan zaben (bayar da dama), amma bai yi watsi da fatan kafa irin wannan tsarin a Nijeriya ba. Ya sake nanatawa cewa, amma wannan ya dogara ne ga idan aka bai wa mutane ‘zabi’ kwatankwacin abin da ya faru a Iran lokacin da aka gudanar da kuri'ar raba gardama wacce ta biyo bayan nasarar juyin juya halin Musulunci na ƙasar a 1979.
Hukumomin Nijeriya sun yarda "a cikin sirri ba a bainar jama'a ba, cewa suna tsoron Harkar Musulunci" da yiwuwar hakan na iya taimakawa wajen kafa "tsarin Musulunci kamar yadda Juyin Juya Halin Musulunci a Iran," in ji shi. Amma gaba daya abin da Harkar Musulunci ke so bayan “shi ne dimokuradiyya. Mene ne dimokuradiyya? Gwamnatin mutane ce. ”
A watan Disambar 2015, rundunar sojin Nijeriya ta kaddamar da wani farmaki a matsayin wani bangare na munanan hare-haren da gwamnatin kasar ta kai wa Harkar Musulunci a Nijeriya wanda Abuja (kotun Abuja) ta bayyana a matsayin haramtacce.
Dangane da halin da jikkunansu ke ciki kuwa, Shaikh Zakzaky ya shaidawa gidan talabijin na Press TV cewa tiyatar da ta biyo baya ta gano birbishin harsasai kusan guda 38 a tsakanin kuncinsa da kan sa, da kuma idanun sa. Ya kara da cewa, matar sa kuma ta samu "harbin bindiga a ciki da cinya."
"Nufin Allah ne cewa ina da rai," in ji Shehin Malamin.
Shaikh Zakzaky ya ce kodayake, binciken da gwamnati ta kira ta hannun gwamnatin jihar kan kisan gillar (Zariya) ba tare da ta shigar da bayanan Harkar Musuluncin ba, amma wani jami'in gwamnati ya shaida cewa "sun binne mutum 347" bayan kawai “kisan gilla daya," in ji shi, ya kara da cewa, "Kuma mun san cewa akwai sauran kisan gillar [suma]. ”
Da ya juya kan batun zaluncin da gwamnati ke yi wa 'yan Shi'a, Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa kaddamar da hari da gwamanti ke yi wa Harkar Musulunci ya faro ne tun shekarun 1970, lokacin da yake dalibi yana yakar akidar gurguzu da kuma akidar rashin yarda da addini.
Ya ce haka aka ci gaba da kai masa hari har cikin shekarun Tamaninoni, inda lokacin aka kama Shehin Malamin kuma aka daure shi har tsawon shekaru hudu. Jagoran ya sake yin wani zaman gidan yari na tsawon watanni tara daga Disamba 1984.
Wasu karin hare-haren guda biyu akan Harkar Musulunci ya sanya an daure shi daga 1987 zuwa 1989 da kuma daga 1996 zuwa 1998.
No comments