Makonni biyu bayan sace Sarkin Bungudu da ke jihar Zamfara, bayanai sun nuna cewa har yanzu ba a ji duriyarsa ba. An sace Alhaji Hassan At...
Makonni biyu bayan sace Sarkin Bungudu da ke jihar Zamfara, bayanai sun nuna cewa har yanzu ba a ji duriyarsa ba.
An sace Alhaji Hassan Attahiru mai daraja ta daya a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja a ranar 14 ga watan Satumba tare da wasu matafiya.
Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta ruwaito cewa maharan sun bukaci iyalan wasu daga cikin wadanda suka sace su kara musu naira miliyan 100, bayan karbar naira miliyan 20 tunda farko.
Sai dai a cewar wata majiyar tsaro babu wasu bayanai game da halin da Sarkin Bungudu Hassan Attahiru ke ciki.
To amma jaridar Trust ta ce Jami'in Hulda da Jama'a na Rundunar 'yan sanda a Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar mata da cewa suna iya kokarinsu na ceto Sarki Hassan Attahiru da sauran matafiya da aka sace shi tare da su.
-BBC Hausa
No comments