Labarin dake shigowa MADOGARA na nuni da cewa; Kannywood ta yi babban rashi na Malam Ahmad Aliyu Tage. Bayanai sun nuna cewa ya rasu n...
Labarin dake shigowa MADOGARA na
nuni da cewa; Kannywood ta yi babban rashi na Malam Ahmad Aliyu Tage.
Bayanai sun nuna cewa ya rasu ne bayan ya yi fama da rashin lafiya wanda ta kai ga har an kwantar da shi a asibitin Nasarawa da ke jihar Kano..
Mujallar Fim ta tabbatar da labarin rasuwarsa. Kazalika rahotannin BBC ya tabbatar da rasuwar tauraron fina-finan Hausa na Kannywood Ahmad Tage.
Tuni 'yan wasan Hausa na Kannywood suka fara mika ta'aziyyarsu a shafukan sada zumunta.
Ya fi fitowa a fina-finan barkwanci a tsawon lokacin da ya kwashe a harkar, wadda ya fara a matsayin mai daukar bidiyo, kafin daga bisani ya rikide ya zama tauraro.
'Yan uwansa sun shaida wa BBC Hausa cewa ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya 21.
No comments