Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Masar Ta Yanke Wa Wasu 'Yan Kasashen Waje 8 Hukuncin Kisa Kan Fataucin Kwayoyi

  Rfi Hausa ta labarto cewa; wata kotu a Masar ta yanke wa wasu 'yan kasashen waje takwas da' yan kasar Masar biyu hukuncin kisa kan...

 


Rfi Hausa ta labarto cewa; wata kotu a Masar ta yanke wa wasu 'yan kasashen waje takwas da' yan kasar Masar biyu hukuncin kisa kan laifin safarar fiye da tan biyu na hodar Iblis ta teku.

A shekarar 2019, Hukumomi suka kwace kwayoyin da aka shigo da su ta Tekun Bahar Maliya, wanda darajarsu ta kai kusan fam biliyan 2.5 (dala miliyan 159).

An yanke wa 'yan Pakistan bakwai,' da yan Masar biyu da wani dan kasar Iran da laifin boye miyagun kwayoyi, ciki har da kusan kilo 100 (fam 220) na methamphetamine, a cikin dakin ajiya da ke cikin jirgin.

Sai dai majiyar shari’ar  ba ta yi cikakken bayani kan inda jigilar kayan ta samo asali ba. .

A kasar Masar da tafi yawan al’umma Larabawa a duniya, ana aiwatar da hukuncin kisa ga farar hula ta hanyar rataya. Za a iya daukaka kara kan hukuncin cikin watanni biyu.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun sha sukar kasar Masar kan karuwar zartar da hukuncin kisa wanda ya ninka har sau uku zuwa 107 a bara, daga 32 a shekarar 2019.

Kasar Masar ce ke aiwatar da hukuncin kisa na uku mafi girma a duniya, bayan China da Iran, a cewar kungiyar Amnesty International.


No comments