Daga Auwal Adam Shugaban ‘Yan kabilar Igbo ta Ohanaeze dake Nijeriya Farfesa George Obiozor ya ce babu yadda za a yi su balle d...
Daga Auwal Adam
Shugaban ‘Yan kabilar Igbo ta Ohanaeze dake Nijeriya Farfesa George Obiozor ya ce babu yadda za a yi su balle daga kasar domin kafa kasar Biyafara kamar yadda wasu suke tunani, domin kuwa babu wata kabila dake cin gajiyar dorewar Nijeriya zama kasa guda fiye da ‘yayan kabilar su.
Shugaban ya kuma ce babu wanda ya isa ya fitar da su daga Nijeriyar duk da matsalolin da kasar ke fuskanta da kuma korafe korafen da kowanne sashe ke yi.
Obiozor ya bayyana cewar ‘Yan kabilar Igbo a Nijeriya kamar kifi ne a cikin teku, saboda haka mutu-ka-raba, domin babu wani tumbatsar ruwan da zai kora su zuwa tudu.
Rfi Hausa ta labarto cewa; shugaban ya ce ‘Yan kabilar Igbo na kowanne sashe na Nijeriya inda suke gudanar da harkokin kasuwanci da sana’oi, abin da ya kai ga jama’a na fadin cewar duk inda kaga babu ‘dan kabilar Igbo toh ka gaggauta barin wurin.
Obiozor ya danganta matsalolin da ake samu a Nijeriya da rashin shugabanci na gari da adalci wajen raba mukamai da dukiyar kasa da kuma rashin daidaito, inda ya bayyana fatar ganin ziyarar da shugaban kasa Buhari ya kai Jihar Imo za ga bude kofar magance wadannan matsaloli.
Shugaban Ohanaeze ya bayyana fatar ganin ziyarar ta bude sabuwar kofar inganta dangantaka tsakanin gwamnatinsa da mutanen yankin tare da daukar matakai akan korafe korafen da suka gabatar, musamman samar da tsaro da bunkasa harkokin tattalin arziki da samar da tashar jiragen ruwa.
No comments