MATSALAR TSARO: Aisha Buhari Ta Caccaki Pantami

 


Uwargidan Shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta wallafa wani faifan bidiyo na Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami yana shessheka kuka a wani darasi da yake gabatarwa a Masallacin Annur dake Abuja, inda ta rubuta cewa; 'A cire tsoro a yi abin da ya dace'.

 Aisha Buhari ta  wallafa wannan sako ne a shafinta na Instagram.

Manazarta na kalla hakan a matsayin maida martani ga Ministan Sadarwar da Tattalin Arzikin Nijeriya dangane da matsalar tsaron da ake fama da ita a Nijeriya duba da yadda ministan ya shahara da yin kuka da caccakar gwamnati a gwamnatocin baya da ba a dama da shi ba a daidai irin wannan lokaci da matsalar tsaro ya ta’azzara.


Post a Comment

0 Comments