Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da amfani da karfin da sojoji suka yi a Guinea wajen kwace ...
Sakatare Janar na Majalisar
Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da amfani da karfin da sojoji
suka yi a Guinea wajen kwace mulki, inda ya bukace su da su gaggauta sakin
shugaban kasar Alpha Conde.
Sanarwar da Guterres ya
gabatar ta ce yana sanya ido akan abin da ke faruwa a Guinea sau da kafa, a yayin
da ya bayyana takaicin #sa na amfani da karfin bindiga wajen kwace iko.
Yanzu haka al'umaran yau da
kullum sun tsaya cik a birnin Conakry, inda aka rufe kasuwanni da manyan
shaguna, bayan sanarwar sojojin kasar wadanda suka yi ikirarin juyin mulki tare
da kama shugaba kasa Alpha Conde, duk da cewa a bangare guda gwamnati ta ce ta
murkushe yunkurin ne.
Hafsan sojin da ya bayyana
a kafar talabijin din kasar ya kuma sanar da rufe iyakokin sama da kasa da kuma
rusa gwamnatin kasar.
No comments