Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori wasu ministocinsa guda biyu da suka hada da ministan noma Alhaji Sabo Nanono da takwaransa na wutar...
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kori wasu ministocinsa guda biyu da suka hada da ministan noma Alhaji Sabo Nanono da takwaransa na wutar lantarki Saleh Mamman.
Kakakin shugaban Femi Adeshina ya tabbatar da korar manyan jami’an guda biyu wadanda ke rike da manyan ma’aikatu a karkashin gwamnatin Buharin, amma ba tare da bayyana dalilin yin haka ba.
Adeshina ya ce an maye gurbin su da ministan muhalli Dr Mohammed Mahmood Abubakar da kuma ministan ayyuka da gidaje Abubakar Aliyu.
Korar ministocin biyu na zuwa ne bayan shekaru biyu da nada su sakamakon sake zaben shugaban kasar a shekarar 2019.
Wadannan ministoci sune na farko da shugaban ya kora tun bayan sake rantsar da shi a karagar mulki.
Sabo Nanono ya fito ne daga Jihar Kano, yayin da Saleh Mamman ya fito daga Jihar Taraba.
‘Yan Nijeriya sun dade sona korafi dangane da yadda ake tafiyar da ma’aikatar noman kasar a karkashin tsohon ministan duk da ci gaban da gwamnati ke ikirari da shi na habaka noma da kiwo.
Yau dokar hana kiwo a kudancin Najeriya ke fara aiki, wani babban koma baya da ake dangantawa da gwamnatin Muhammadu Buhari.
A bangaren samar da wutar lantarki kuma, ‘yan Nijeriya sun dade suna gabatar da korafi akan yadda ake tatsar su kudade ba tare da samun isasshiyar wutar da suke samu ba.
Rahotanni sun ce yau aka shirya fara aiki da karin farashin wutar a Nijeriya duk da karancin ta a wasu sassa.
No comments