Daga Auwal Adam Kungiyar kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen jihar Gombe ta kira ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pa...
Daga Auwal Adam
Kungiyar
kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen jihar Gombe ta kira ministan sadarwa da
tattalin arzikin zamani, Dr Isa Ali Pantami da cewa dan ta ne mai albarka kamar
yadda Jaridar SaharaReporters ta ruwaito.
CAN
din ta bayyana hakan ne a cikin wata wasika wacce Sakataren kungiyar, Senior
Apostle John Adedigba ya sanya hannu a madadin duk sauran ‘yan kungiyar inda ya
kira Pantami da cewa dan su ne kuma suna alfahari da kasancewarsa dan su.
Kungiyar
har wala yau ta taya Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami farin cikin samun karin matsayin
zuwa daraja ta Farfesa a harkar tsaron yanar gizo.
CAN
ta jihar Gombe ta kara da bayyana yadda Farfesa Isa Ali Pantami ya samu tarin
nasarori daga hawansa kan mulki zuwa yanzu inda ta bayyana alfaharin da take yi
da shi.
No comments