Mutane Da Dama Sun Tsere Daga Gidan Yari A Kogi

 Daga Ammar Muhammad

Gomomin fursunoni ne suka tsere daga gidan gyaran hali na gwamnatin Tarayya dake garin Kabba ta jihar Kogi bayan da wadansu mahara da ba a san ko su wane ne ba suka fasa gidan yarin.  

Lamarin ya auku ne a tsakanin dare ranar Lahadi da safiyar yau Litinin, kamar yadda rundunar ‘yan sanda suka labarta a yayin tabbatar da balle gidan yarin.

Fursunoni da dama da ba a tantance adadinsu ba ne suka tsere daga gidan gyaran halin a Kabba dake karamar hukumar Kabba/Bunu ta jihar inji ‘yan sanda. 

Mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda shiyya ta 8, Ayuba Edeh, a yayin da yake tabbatar da batun fasa gidan yari a ranar Litinin ya ce, Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kogi, Idrisu Dauda da sauran shugabannin Hukumomin tsaro tuni suka dauki matakan da suka dace domin dakile lamarin. 

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kai hari gidan yarin ne dake babban titin Kabba zuwa Lokoja tun daren ranar Lahadi har zuwa safiyar ranar Litinin.

Bayanai sun nuna cewa maharan sun sha karfin jami’an sojin da suke gadi a titin da ke isa gidan yari a lokacin, kafin daga bisani suka kai hari gidan yarin. 

Maharan sun kuma farmaki jami’an gidan gyari kafin daga bisani suka saki fursunonin kamar yadda rahotanni suka labarta. 


Post a Comment

0 Comments