Akalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu a wani artabu tsakanin kungiyoyin asiri a karamar hukumar Gboko ta jihar Binuwe a ranar Laraba. W...
Akalla mutum hudu ne suka rasa rayukansu a wani artabu tsakanin kungiyoyin asiri a karamar hukumar Gboko ta jihar Binuwe a ranar Laraba.
Wani shaidar gani da ido, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa wasu kungiyoyin asiri guda biyu ne masu hamayya da juna suka gwabza fada da neman iko a yankin kuma hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane hudun da ake kyautata zaton membobin kungiyoyin asiri ne.
Ta ce an kama mutane uku da ake zargi da hannu a kisan.
Ta kara da cewa ana ci gaba da bincike kuma za a gurfanar da wadanda aka samu da laifi bayan haka.
No comments