Rahotanni daga Kaduna na cewa mutum 51 suka rasa rayukansu a rikicin kwanaki biyu a yankunan Kudancin Kaduna. Akwai rahotannin da ke cewa ...
Rahotanni daga Kaduna na cewa mutum 51 suka rasa rayukansu a rikicin kwanaki biyu a yankunan Kudancin Kaduna.
Akwai rahotannin da ke cewa an rika kai hare-haren ramuwar gayya musamman a yankin Zangon Kataf, da suka yi sanadin salwantar rayukan fararen hula da ba su ji ba su gani ba.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin kare hakkin bil'adama ke zargi kungiyar gwmanonin Arewa ta Northern Governors Forum da kin cewa komai kan kashe-kashen da ke faruwa a Kudancin Kaduna
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa an kashe akalla mutun 48 a dan tsakanin nan biyo bayan hare haren 'yan bindiga a yankin.
No comments