Fittaciyar jarumar masana’antar Kannywood Hadiza Aliyu Gabon, ta bayyana yadda ta kamu da matsanaicin soyayyar Ministan Sadarwa Sheikh Isa...
Fittaciyar jarumar masana’antar Kannywood Hadiza Aliyu Gabon, ta bayyana yadda ta kamu da matsanaicin soyayyar Ministan Sadarwa Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami.
Jarumar wadda mahaifiyarta Æ´ar asalin jihar Adamawa ce daga Mubi mahaifinta kuma É—an Æ™asar Gabon, ta ce ta Æ™ara jin ta kamu da matsanaicin son Malamin ne tun bayan wani bidiyonsa da ta kalla yana lacca a jami’ar musulunci dake birnin Madina na Æ™asar Saudiyya.
Hadiza Gabon wacce ake wa laÆ™abi da uwar marayun Kannywood, na daga cikin jarumar masana’antar mata attajirai, ta kuma ce ba kuÉ—in Malamin ne ya ja hankalinta ba, domin a wadace take. Ta shaida cewa a shirye take a kowani lokaci ta daina yin fim idan har Sheikh Pantami zai aure ta, kamar yadda Neptune Prime ta ruwaito.
A cikin wani gajeren bidiyon da ta É—ora a shafinta kuma yake yawo a shafukan Instagram da Facebook, ta yi alÆ™awarin zama mace tagari, mai addini da bin Æ™a’odojin mijinta har da zama matar kulle idan Pantami ya buÆ™aci hakan.
Ta ce bata da wani babban buri a yanzu da ya wuce ta yi aure ta haifi Æ´aÆ´a kuma Sheikh Pantami ne burinta kuma shi take ta yin mafarkin ta zama matarsa a Æ´an kwanakin nan.
-Hausa Daily Times
No comments