Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa; sakamakon lugudan wuta da jami’an tsaro ke yi wa ‘yan bindiga a dazukan jihar Zamfara, sun turo...
Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana cewa; sakamakon lugudan wuta da
jami’an tsaro ke yi wa ‘yan bindiga a dazukan jihar Zamfara, sun turo wasu
manyan mutane zuwa ga Gwamna Bello Matawalle suna tuba da neman sulhu. Gwamna Matawalle ya amsa masu da cewa, an kulle karbar tubar
su, lugudan wuta yanzu aka fara.
Gwamna
Matawalle ya bayyana haka bayan kammala sallar Juma’a a Masallacin Sabo dan
Ashafa da ke Gusau.
Matawalle
ya kara da cewa, a ranar Alhamis da ta gabata an turo Kwamitin Babba daga
Garuruwan Mada, Ruwan Baura da Acha; “kan in zagaita wuta, sun tuba, na ce na
rufe hanyar tuba ga Barayi ‘yan ta’adda , wallahi ba zan tsagaita ba, lokacin
da muka nemi su tuba, su kaki. Kuma mun bi duk hanyar da ta dace a bi sun ki
sai yanzu da suka ji wuta, don haka tsakaninmu da su sai mu hadu wajen
Ubangijinmu”, Inji gwamna Matawalle kamar yadda Jaridar LEADERSHIP Hausa ta
labarto.
Gwamna
Matawalle ya kuma yi kira ga al’ummar jihar Zamfara da su ci gaba da bada hadin
kai.
Kuma
ya gargadi ‘yan siyasa da su daina ba mutane manyan Mashina masu amfani da kuloch,
dan idan an ba su ne suke saidawa, sai barayi su saya su rika amfani da su a
cewarsa.
“Don
haka duk dan siyasa da muka kama yana bada irin wadannan Mashina lallai zamu
hukun tashi”, inji Gwamna Matawalle.
No comments