Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta kwace wata babbar mota dauke da madarar da ba a yi wa rijista ba da ake zargi jabu...
Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) ta kwace wata babbar mota dauke da madarar da ba a yi wa rijista ba da ake zargi jabu ce a Sakkwato.
Kodinetan NAFDAC ta jihar Sakkwato, Malam Garba Adamu ne ya bayyana hakan a wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Laraba a Sakkwato.
Adamu ya ce, an kwace katan 300 na jakar ‘cream 35g’ a ranar 6 ga Satumba a shahararriyar kasuwar Kantin Daji yayin da motar ke kan hanyar zuwa Kano.
Ya ce an kwace kayayyakin kuma an ci tarar mutanen da abin ya shafa, domin su zama abin izina ga wasu.
Kodinetan ya yi bayanin cewa hedkwatar hukumar a cikin watan Yuli, ta sanar da ofisoshin jihohi na yada madarar da ba a yi wa rijista da sauran kayayyaki a cikin kasar.
Ya umarci jama’a da su yi taka tsantsan da abubuwan da suke amfani da su tare da sanya ido kan duk wani abu da ba a yi wa rijista ba don tallafa wa NAFDAC wajen kare lafiyarsu.
No comments