Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

NAZARI: Anya Facebook Dandalin Sada Zumunta Ne?

  Daga Ibraheem El-Tafseer Kafar sadarwa ta Facebook, ɗaya ne daga cikin kafofin sadarwa na zamani wanda ake yaɗa saƙonni a soshiyal mid...

 


Daga Ibraheem El-Tafseer

Kafar sadarwa ta Facebook, ɗaya ne daga cikin kafofin sadarwa na zamani wanda ake yaɗa saƙonni a soshiyal midiya cikin gaggawa. Facebook, ɗaya ne daga cikin 'applications' (manhajoji) dangogin su Twitter, Instagram, Telegram, Snapchat da sauransu. Kamar a Nijeriya kam, Facebook ya fi shahara a yanzu, tun da an rufe kafar sadarwa ta Twitter.

Ana yiwa Facebook laƙabi da kafar sada zumunta. Tun da a Facebook ana iya haɗuwa da mutanen da ba a sansu ba, kuma a ƙulla alaƙa mai ƙarfi, har ta kai an ziyarci juna, daga nisan garuruwa. Facebook yana haɗa zumunci sosai, sannan yana raba zumunci sosan gaske.

Nasan ba sabon abu bane, haɗuwa ta dalilin Facebook har a ziyarci juna daga nisan jihohi a faɗin Nijeriya. Wannan ya sha faruwa, akwai dalilai da yawa kan haka. Kuma zumunci ya ƙullu yadda har idan wani abin farin ciki ko na baƙin ciki ya faru da ɗaya, sukan ziyarci juna.

Facebook yana haɗa zumunci tsakanin namiji da mace har ya kai ga sun yi aure. Ni ma akwai abokina da dalilin Facebook suka haɗu da matar da ya aura, kuma har yanzu suna tare. Facebook yana haɗa abubuwa da yawa har da baɗala.

Akwai group-group ɗin na sada zumunta da yawa a Facebook, wanda ya haɗa mutane da dama, maza da mata, ana kuma sadar da zumunta ɗin. Misalin ɗaya daga cikin irin waɗannan group ɗin shi ne group ɗin 'Home Of Solace' wanda ko a watannin baya sun shirya taro, kuma da yawa daga cikin 'yan group ɗin sun halarta, an ci, an sha, an yi raha, sannan aka ɗauki hotuna. Zumunci ya ƙullu tsakanin da dama daga cikinsu.

Facebook wani wuri ne da mutane suke rubuta ra'ayoyinsu da nufin isar da saƙo, cikin harsunan da suke buƙata saƙon ya isa. Kamar mu a nan Nijeriya, an fi yin rubutun da yarukan Hausa, Turanci, Larabci da Faransanci. Da farko idan mutum ya buɗe shafin Facebook, akwai buƙatar yasan da wane dalili ya buɗe shafin Facebook ɗin.

Idan saƙo yake so yana isarwa, to sai ya duba ya ga da wane yare ya kamata ya yi rubutu wajen isar da saƙon, domin saƙon ya isa ga wanda aka yi dominsu. Wasu suna hawa Facebook ne don su karanta labarai da sauransu. Wasu kuma suna hawa Facebook ne don su ci mutuncin wasu.

Akwai Gidauniyoyi (Foundations) na neman taimako da yawa da suke sako hotunan waɗanda ake nema wa taimakon a shafukansu na Facebook. Kuma tabbas ana samun taimakon sosai a Facebook ɗin. Akwai misalai da yawa kan haka. Hajiya Fauziyya D. Sulaiman ɗaya ce daga cikinsu.

Facebook ya kasance wajen samun labarai cikin gaggawa. Kusan dukkan kafafen yaɗa labarai na jaridu da gidajen Talabijin da Rediyo duk suna da shafi a Facebook wanda suke wallafa labaransu a ciki. Da zarar labari da ɗumi-ɗumi ya samu, za ka ga suna ta rige-rige wajen wallafa wa a shafukansu. Hakan yasa mafi yawan labarai a Facebook ake fara gani, kafin a samu cikakken labarin daga baya.

Facebook ɗin kuma ya shahara wajen kawo labarai na ƙanzon kurege, shiyasa da yawan mutane basa yarda da labaran Facebook, har sai sun ga wata jarida ta gaske ta wallafa labarin a shafinta. Abin da ya sa nace jarida ta gaske shi ne, jaridun bogi suna nan birjik a Facebook. Da zarar mutum ya sayi babbar waya, to shi ma ya zama ɗan jarida. Abin da yake ta faruwa kenan yanzu a Facebook da WhatsApp.

Wasu kuwa suna hawa Facebook ne don ganin labaran ban dariya (comedy), don nishaɗi da rage damuwa. Wasu kuma fasadi kawai suke yaɗa wa a Facebook. Ko kunya babu za ka ga suna ta furta kalaman batsa da rashin tarbiyya iri-iri a bidiyo su xora a Facebook da sunan tallan magani ko kuma yaɗa iskanci.

Haka kuma Facebook ya zama wajen hada-hadar kasuwanci iri-iri. Kusan dukkan masu manyan masana'antu, da masu manyan shaguna har da masu matsakaitan kasuwanci, duk suna da shafuka da suke tallata harkokin kasuwancinsu ta hanyoyin rubuce-rubuce a Facebook, haɗe da hotuna da Bidiyon yadda kasuwancin nasu yake.

Sannan Facebook ya zama wajen sanar da saƙonnin aure, suna da mutuwa. Zai wahala garin Allah ya waye, ba ka ga an sanar da ɗaya daga cikin ukun nan ba. Dalilin Facebook yasa an daina buga katin aure barkatai da ake yi a shekarun baya.

Facebook ya zama wajen yaɗa manufofin 'yan Siyasa. Kowace jam'iya tana da nata shafin a Facebook domin yaɗa manufofin ta. Duk wani babban ɗan siyasa yana da nasa yaran masu tallata manufofinsa da ayyukansa a Facebook.

Haka za ka yi ta kallon hotunan 'yan Siyasa daga ko ina a faɗin ƙasar nan. Wani daga an ɗora hotonsa rikici zai ɓarke a wajen 'comments' a yi ta zage-zage da cin mutuncin juna. Mummunar gaba ta ƙullu tsakanin masoyan jam'iyyun, su kuma 'yan siyasar babu ruwansu. Sai dai ma a nuno su sun haɗu a wajen wani taro suna gaisawa da juna har suna dariya da raha.

Akwai kuma waɗanda suka ɗauki Facebook tamkar makaranta, suna ƙaruwa matuƙa da rubuce rubucen da wasu suke yi, na addini da kuma masu yin sharhi kan al'amuran yau da kullum. Akwai waɗanda kullum da ka ga rubutunsu a Facebook, to wa'azi ne ko nasiha. Irin waɗannan sune suka fi kaɗan.

Akwai waɗanda suka ɗauki Facebook wajen cin mutuncin jama'a, su zagi wanda suke ƙi, su ci mutuncinsa, su ɓata masa suna, saboda wata manufa ko bambamcin fahimta na addini ko bambamcin ra'ayi na siyasa. Irin wannan shi ya fi yawa sosai a Facebook yanzu.

Akwai waɗanda suka daina buɗe shafinsu na Facebook saboda irin cin mutuncin da ake yiwa jama'a, musamman Malaman addini. Duk girman Malami za a iya ƙunduma masa ashar.

A Facebook ne za ka ga an ɗauko hoton Malamin addini an jirkita masa kama an yi amfani da 'Photoshop' an nuna shi cikin wata mummunar kama, ko  kuma ma a nuna siffarsa haɗe da wata dabba. A Facebook ne za ka ga jahili, wanda bai taɓa shiga aji ba, yana kiran babban Malamin addini da jahili ko mahaukaci, saboda tsantsar ƙiyayya ko kuma saɓanin fahimta.

A Facebook ne ɗan Sakandire zai kira Malamin da ya yi digirin-digirgir (PhD) da jahili, saboda bambamcin ra'ayi. A Facebook sam wasu ba sa ganin kima da darajar mutane, ko waye za su iya ci masa mutunci, su ƙunduma masa ashar.

A Facebook ne saboda ana buƙatar a baƙanta mutum, musamman Malaman addini, sai a ɗauki tsoffin jawabansa da sabbi a yayyanke, a jojjona inda ake so, don fitar da wata mummunar manufa, don a ɓata masa suna, ya faru da yawa mun gani.

Facebook ya zama wajen yaɗa ƙarerayi, ƙazafi, ƙage da sharri. Akwai waɗanda suka ɗaukarwa kansu haka, kullum abin da suke yaɗa wa kenan a Facebook. A Facebook ne ake ƙirƙirar labarin da babu shi, kuma a yi ta yaɗa shi, sai daga baya a gano labarin bashi da asali ballantana tushe. Labarin ƙanzon kurege kam ya zama ruwan dare a Facebook.

Ko a makon da ya gabata, an yi ta yaɗa cewa tsohon ministan wutar Lantarki, Saleh Mamman wai ya yanki jiki ya faɗi, a lokacin da ya samu labarin an tsige shi. Da 'yan Jarida suke tambayarsa kan haka, sai yace shi ma a Facebook ya gani ana ta yaɗa wa, amma ƙarya ake masa, shi kam bai faɗi ba. Shi ma bai san daga ina labarin ya samo asali ba.

A Facebook ɗin nan dai za ka ga Hausawa, 'ya'yan musulmai suna ɗora hotunansu, wanda bashi da maraba da tsirara, suna tallata kansu ga jama'a. Abin mamakin sai ka ga wasu maza masu irin budurwar zuciya ɗin nan, suna ta yaba musu hotunan, su kuma suna jin daɗi. Wanda hakan ya saɓa da koyarwar addinin Musulunci da kuma al'adar Bahaushe.

Yadda wasu suke rubuta abin da suka ga dama a Facebook, da sunan 'yancin faɗin albarkacin baki (Freedom of Expression). Su zagi wanda suke ƙi, su yi ƙarya, ƙage da ƙazafi ga wasu mutanen da suke da bambamcin fahimta a addini ko a siyasa. Wasu iyayen gidansu ne suke saka su, wasu kuma ra'ayin kansu ne.

To yana da kyau mutum ya sani, a duk lokacin da za ka yi rubutu a Facebook ko kuma rubutu a ko ina, to ka tuna cewa Allah zai tambayeka a kan wannan rubutun. Duk abin da ka rubuta, Allah zai tayar da kai, a ranar Lahira, ya maka tambaya a kan abin da ka rubuta. Lallai a yi taka tsantsan wajen rubuta abin da mutum ya san ba gaskiya bane.


No comments