Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ja kunnen shugaba Muhammadu Buhari kan shirinsa na sake karbo sabbin basuka, yana mai cewa y...
Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya ja kunnen shugaba Muhammadu Buhari kan shirinsa na sake karbo sabbin basuka, yana mai cewa yin aro don tara bashi ga Æ´an gobe babban laifi ne.
Da yake magana da gidan Talabijin na Channels a gefen wani taro a Afirka ta Kudu, Obasanjo ya ce cin bashin da ake yi sannan ake kin biyan wanda ake bin kasar na iya zama gagarumar matsala ga gwamnacin da za su zo a gaba.
Ko da yake ya ce cin bashi ba matsala bane, tsohon shugaban ya bayyana cewa abin da zai iya zama matsala shi ne biyan bashin.
''Idan ana ciyo bashi don aiwatar da ayyukan da za su iya biyan kudinsu ne to wannan ba matsala bane, idan kuwa don aiwatar da ayyukan al'amuran yau da kullum ne to wannan babbar wauta ce'' inji Obasanjo.
No comments