Jam'iyyar adawa ta PDP ta caccaki jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya kan marawa kalaman gwaman Babban bankin kasar wato CBN baya, kan y...
Jam'iyyar adawa ta PDP ta caccaki jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya kan marawa kalaman gwaman Babban bankin kasar wato CBN baya, kan yada darajar naira ke ci gaba da faɗuwa.
A wata sanarwa da PDP ta fitar dauke da sa hannun Sakatarenta na kasa Kola Ologbondiya, ta ce kalaman Godwin Emefiele zagon-kasa ne ga tattalin arziki da kuma sake jefa rayuwar 'yan Nijeriya cikin matsanancin yanayi.
PDP ta zargi cewa APC na amfani da gwamnan CBN wajen rarraba da wawushe dukiyar kasa.
Jam'iyyar ta yi kira ga APC da gwamnatin shugaba Buhari ta fito ta gyara aika-aikanta da suka jefa naira cikin mawuyancin yanayi da kuma tabbatar da adalci da ayyuka a bayyane.
No comments