Shugaban La Ligar Spain, Javier Tebas, ya yi ikirarin cewa Real Madrid tana da isassun kudin da za ta iya sayen Kylian Mbappe da Erling Ha...
Shugaban La Ligar Spain, Javier Tebas, ya yi ikirarin cewa Real Madrid tana da isassun kudin da za ta iya sayen Kylian Mbappe da Erling Haaland a shekara mai zuwa.
Tebas ya bayyana haka ne a wata ganawa da manema labarai a ranar Litinin.
Real Madrid din dai ta gaza a kokarin da ta yi ta yi na sayen Mbappe daga Pafris Saint Germain a watan da ya gabata.
Har sai da kungiyar ta LaLiga ta ta yi tayin bada fam miliyan 137 amma PSG ta yi fatali da wannan tayi.
Madrid ta kara kudin zuwa fam miliyan 145 har da wasu jerin kari da suka kai fam miliyan 9 jimilla, amma duk da haka PSG din ta ce ba ta san wanna zance ba.
A ranar karshe ta kasuwar hada hadar ‘yan wasa, Madrid ta kara tayin baiwa PSG fam miliyan 189 a kan Mbappe din amma sai ta ji shuru daga kungiyar ta kasar Faransa.
No comments