Real Madrid Ta Fara Wasa Da Kafar Dama A Santiago BernabeuReal Madrid ta yi nasarar doke Celta Vigo da ci 5-2 a wasan farko da ta buga a Santiago Bernabeu, tun bayan kwana 560.

Real wadda ta karbi bakuncin Celta a karawar mako na hudu a gasar La Liga, an far zura mata kwallo a raga ta hannun Santi Mina minti hudu da fara wasa, daga baya ta farke ta hannun Karim Benzema.

Celta ta kara kwallo na biyu ta hannun Franco Cervi daga baya Karim Benzema ya kara farke mata, sannan Vinicius Junior ya ci mata na ukun.

Sabon dan kwallon da Real Madrid ta saya a bana daga Rennes wanda ya canji Eden Hazard, Eduardo Camavinga ne ya ci na hutu a wasan farko da ya fara buga wa Real Madrid.

Saura 'yan minti biyu a tashi daga karawar Karim Benzema ya kara na biyar a bugun daga kai sai mai tsaron raga, kuma na uku rigis da ya ci Celta Vigo a ranar ta Lahadi

Rabonda a taka leda a filin Santiago Bernabeu tun ranar 1 ga watan Maris din 2020 a lokacin da Real Madrid ta doke Barcelona a karawar El Clasiso.

Bayan kammala karawar an zabi Benzema a matakin wanda ya fi taka rawar gani a wasan na mako na hudu.

-BBC Hausa

Post a Comment

0 Comments