Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Salah Ya Shiga Jerin 'Yan Wasan Firimiya Da Suka Zura Kwallo 100

  Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya kafa tarihin zama dan wasan Firimiya na 30 da ya yi nasarar zura kwallaye 100 yayin karawar k...

 


Dan wasan gaba na Liverpool Mohamed Salah ya kafa tarihin zama dan wasan Firimiya na 30 da ya yi nasarar zura kwallaye 100 yayin karawar kungiyar tasa da Leeds United jiya lahadi.

Salah dan Masar wanda wasan na jiya shi ne na 162 da ya dokawa Liverpool tun bayan sayo shi daga Roma a shekarar 2017, mai horar da tawagar Jurgen Klopp ya bayyana shi a matsayin guda cikin jajirtattun ‘yan wasa da kungiyar ta yi a tarihi.

An dai ta shi wasan na jiya Liverpool na da 3 Leeds na neman bayan kwallaye daga ‘yan wasanta Mo Salah, Fabinho da kuma Sadio Mane, matakin da ya mayar da Liverpool ta 3 a teburin firimiya amma maki kankankan da jagora Manchester United da kuma Chelsea da ke matsayin ta 2.

Yayin wasan na jiya dan wasan baya na Liverpool Harvey Elliott ya gamu da rauni bayan takawar da mai tsaron bayan Leeds, Pascal Struijk ya yi masa.

An dai baiwa dan wasan na Leeds jan kati, yayinda aka yi waje da Elliot saboda raunin daya tsananta tare da maye gurbinsa da Kaftin Jordan Henderson.

No comments