Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sama Da Dalibai Dubu Daya Ne ‘Yan Bindiga Suka Sace A Makarantu A Shekarar Nan -Rahoto

  Fiye da dalibai dubu 1 ne aka sace a daga makarantun Nijeriya a wannan shekarar, a cewar Save the Children, wata kungiya mai zaman kanta. ...

 


Fiye da dalibai dubu 1 ne aka sace a daga makarantun Nijeriya a wannan shekarar, a cewar Save the Children, wata kungiya mai zaman kanta.

Daraktar kungiyar a Najeriya, Mercy Gichuhi ce ta bayyana haka a wata sanarwa na bikin ranar kare ilimi daga hare hare ta biyu.

Kungiyar ta ce ta’azzarar da satar yara ‘yan makaranta ta yi a tsakanin shekarar 2020 da 2021 ne ma ta tilasta rufe makarantu, lamarin da ya jefa tsarin ilimin kasar cikin hatsari.

Sanarwar da kungiyar ta fitar ta ce daga watan Janairu zuwa Agustan shekarar 2021, sama da yara dubu 1 ne aka yi garkuwa da su, inda da dama daga cikinsu ke hannun masu garkuwar har yanzu.

Kafafen yadda labaran Najeriya sun ruwaito sau da dama labarin hare haren ‘yan bindiga a kan makarantu a jihohin Kaduna Katsina, Kebbi, Zamfara da Neja, inda aka sace daruruwan yara don neman kudin fansa.

No comments