Daga Wakilinmu Sama da Naira Miliyan 345 ne aka nema aka rasa a Asusun Kotun Shari’a ta Kano kamar yadda gidan Rediyon Freedom suka labart...
Daga Wakilinmu
Sama da Naira Miliyan 345 ne aka nema aka rasa a Asusun Kotun Shari’a ta Kano kamar yadda gidan Rediyon Freedom suka labarto.
Babban Alkalin jihar, Tijjani Yakasai ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce tuni aka kai rahoton lamarin gaban Hukumar karbar korafe-korafen al’umma da yaki da cin hanci ta jihar Kano, PCACC domin gudanar da bincike.
Sakataren kotun, Haruna Khalil, ya ce an kafa kwamitin bincike kan batun.
A cewarsa kudin ma marayu ne da aka ajiye a kotun kafin a kai ga bayar da shi ga masu hakki.
A cewarsa murfin ya bude ne a daidai lokacin da kotu ta yi kokarin cire wani bangare na kudin, sannan ta gano cewa Naira miliyan 9 kacal ya rage a cikin asusun.
Bayanai sun nuna cewa bayan kafa kwamitin bincike, an sake wadansu na’urorin kwamfuta a Hukumar domin rufe abubuwan da suka wakana.
Mukaddashin Hukumar karbar korafe-korafen al’umma da yaki da rashawa ta Kano, Mahmud Balarabe, ya ce sun gayyaci kafatanin wadanda suke da hannu a ciki tare da jami’an Bankin domin yi musu tambayoyi.
No comments