Wadansu daga cikin iyalan wadanda sojoji suka kashe a Zariya a watan Disambar 2015 sun gana da jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Z...
Wadansu daga cikin iyalan wadanda sojoji suka kashe a Zariya a watan Disambar 2015 sun gana da jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky a ranar Lahadin 19 ga watan Disambar 2021 a gidansa dake Birnin Tarayya Abuja.
Shehin Malamin ya yi amfani da wannan damar na ganawa da bakin da aka gayyata domin jajanta musu da mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan bisa rashin masoyansu da suka yi. Inda ya karfafe su da cewa a koyaushe su rika tunawa da irin zaluncin da wahalhalun da aka yi wa Imam Hussaini (AS) a yayin da rundunar Yazidu ta yi musu kisan kiyashi.
Ya nusasshe da wadanda suka ziyarce shi cewa; babu sadaukarwa da ta yi yawa a tafarkin Allah.
Wakilin MADOGARA da ke wajen ziyarar ya labarto mana cewa; Shaikh Zakzaky har wala yau ya bada hakuri bisa gayyatar wadansu daga ciki, a maimaikon ya bi su gida-gida ya jajanta musu. “sakamakon raunukan da ke jikinmu wanda muka samu a yayin harin da sojoji suka kawo mana, har yanzu akwai birbishin harsashi a jikinmu, kuma babu hanyar da zamu hadu da dukkanin wadanda abin ya shafa da wadanda suka tsira daga harin ta’addancin sojoji akanmu a Disambar 2015”, ya jaddada.
Da yake maida bayani, daya daga cikin iyayen wadanda suka rasa ‘ya’yansu, Mallam Isa Waziri Gwantu wanda ya rasa ‘ya’yansa hudu a yayin kisan kiyashin na Zariya, ya bayyana godiyarsu ga Shehin Malamin bisa gayyatar su da ya yi a irin wannan mawuyacin hali, inda ya jaddada aniyarsu na cewa komin wuya ba za su yi watsi da tafarkin gaskiya da Shehin Malamin yake yi wa jagoranci ba.
Kazalika, Hajiya Jummai Karofi, wacce ta rasa ‘ya’yanta biyar sakamakon harin da sojoji suka kai wa Harkar Musulunci a Zariya, ta kara da cewa, za ta so wadanda suka kashe ‘ya’yansu da iyalinsu su sani cewa abin da suka aikata musu ba zai taba tsoratar da su ba daga barin Shaikh Zakzaky da Harkar Musulunci a Nijeriya. A cewarta a hakikanin gaskiya a shirye suke su biya mafi girman sadaukarwa wajen kare Musulunci.
Daga karshe Shaikh Zakzaky ya roki Allah Madaukakin Sarki ya bai wa iyalan shahidai karfin guiwa da juriya wajen jure rashin da suka yi wanda ba za a iya mayar wa ba wanda sojoji suka aikata.
Ya yi addu'ar Allah ya karbi shahadar wadanda sojoji suka kashe.
No comments