Shugaba Buhari Na Son Majalisa Ta Bashi Dama Ya Ranto Bashin Kusan Triliyan 2

 


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya buƙaci majalisar dokokin ƙasar ta bashi dama ya ranto Naira 1,668, 417, 229, 124.5, wato Naira Triliyan daya da biliyan dari shida da sittin da takwas da miliyan dari hudu da goma sha bakwai da motsi.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa shugaban ya ce za a yi amfani da kudin ne domin aiwatar da kasafin kudin kasar na shekarar 2021.

Cikin wata wasika da shugaban ya aika wa majalisar dokokin kasar, ya ce bashin wani bangare ne na shirin yin rance, da aka tsara tun shekarar 2018 zuwa 2020.

Ya ƙara da cewa ciyo bashin ya zama dole, domin cimma burin aiwatar da wasu ayyuka da za su amfani jama'ar kasar.


Post a Comment

0 Comments