Shugaba Buhari Ya Amince Da Nadin Farfesa Yusuf A Matsayin Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Nijeriya

       Farfesa Yusuf Aminu Ahmed a hagu. 

Daga Auwal Adam 

Shugaban kasa, Muhammad Buhari ya amince da nadin Farfesa Yusuf Aminu Ahmed a matsayin Shugaba kuma Babban Darakta na Hukumar Makamashin Nukiliya ta Nijeriya (NAEC) wanda zai fara aiki daga watan Satumbar 2021. 

Babban Sakataren Ayyuka Dr. Nnamdi Maurice Mbaeri, OSGF ne ya mika wa Farfesa Ahmed wasikar fara aikinsa.

A wata sanarwar manema labarai da Willie Bassey, Daraktan yada labarai na Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya fitar a yau Juma'a, wacce MADOGARA ta samu kwafenta, an tabbatar da cewa shugaban kasa ya amince da nadin Farfesa Yusuf Aminu Ahmed a matsayin shugaban hukumar har na tsawon shekaru uku kamar yadda doka na 4 sakin layi na 1 na dokokin Hukumar Makashin Nukiliya ta Nijeriya ta tanada ta 1976. 

Nadin na shi a cewar sanarwar zai fara aiki ne daga ranar 3 ga watan Satumbar 2021. 

Har zuwa lokacin nadinsa, Farfesa Yusuf Aminu Ahmed ya kasance Babban Darakta a Ofishin Shugaban Hukumar Makamashin Nukiliya ta Nijeriya. 

Ya kasance Farfesa ne a Kimiyyar Nukiliya wanda ya kwashe shekaru yana bincike na shekaru a bangaren Nukiliya. 

An kafa Hukumar Makamashin Nukiliya ta Nijeriya ne a shekarar 1976 bisa manufar ginawa da kuma kula da cibiyoyin makamashin nukiliya da nufin samar da wutar lantarki, gudanar da bincike kan batutuwan da suka shafi amfani da makamashin nukiliya cikin lumana tare da ilmantarwa da kuma horas da mutane kan batutuwan da suka shafi makamashin Nukiliya da sauran abubuwa. 

Post a Comment

0 Comments