Shugabajn kasa Muhamamdu Buhari ya zargi ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty da goyon-baya ta'addanci da ake aikatawa a ƙasar. S...
Shugabajn kasa Muhamamdu Buhari ya zargi ƙungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty da goyon-baya ta'addanci da ake aikatawa a ƙasar.
Shugaban a wata sanarwa É—auke da sa hannun kakakinsa Malam Garba Shehu ya ce Amnesty wacce doka ba ta bata damar gudanar da ayyukanta a Nijeriya ba, a yanzu haka ta jefa siyasar cikin gida a lamuranta a cewarsa.
Shugaba Buhari ya zargi ofishin Amnesty na Nijeriya da neman farantawa wasu tsiraru da kira ga ƙungiyar ta binciki ayyukan jami'anta a Abuja.
Sanarwar dai ta ce Amnesty na kankamba a wasu batutuwan tsaron cikin gida da kare jagoran 'yan awaren IPOB wanda a dalilisan mutane da dama suka rasa rayukansu a Nijeriya.
Sannan ya ce ana amfani da Amnesty wajen rufe manyan laifuka, kuma wannan yanayi ne na Alla-wadai da ake gani a wata kasa ta Afirka.
No comments