Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Shugaba Buhari Zai Tallafawa Kasar Burundi Ta Samu Ci Gaba

  Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa Nijeriya za ta taimakawa kasar Burundi a wani mataki na kokarin da ake yi na inganta z...

 


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin cewa Nijeriya za ta taimakawa kasar Burundi a wani mataki na kokarin da ake yi na inganta zaman lafiya da ci gaba a kasar da ke Kudancin Afirka.

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Mista Femi Adesina, ya fitar a ranar Talata, ta ce shugaban ya yi wannan alkawarin ne lokacin da ya gana da Shugaba Evariste Ndayishimiye na Jamhuriyar Burundi.

An gudanar da taron ne a gefen iyakar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76 da ake yi a New York ta kasar Amurka, a ranar Talata.

“Za mu kasance masu kwazo da bayar da tallafi gwargwadon iyawarmu,” in ji Shugaba Buhari.

Shugaban na Burundi ya ba da tabbacin cewa kasarsa na cikin rikici, “yanzu akwai zaman lafiya da sulhu kuma muna da dimbin damar amfani.”

Ya ce kasar sa na neman goyon bayan kasashen domin sada zumunci a fannonin samar da mai, ayyukan gona, ma’adanai, da sauran su da dama, wanda kwararrun Najeriya za su iya bayarwa.


No comments