Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Shugaban EFCC Ya Yanke Jiki Ya Fadi A Fadar Shugaban Kasa A Abuja

Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin zagon kasa Abdulrasheed Bawa, an yi gaggawar fice wa da ...



Shugaban Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin zagon kasa Abdulrasheed Bawa, an yi gaggawar fice wa da shi daga Fadar Shugaban Kasa dake Abuja, bayan ya fadi a wani a wani taro dake gudana a yau Alhamis.

Bawa na jawabin fatan alheri ne, a Taron Ƙasa, sai kwatsam akaji ya daina magana.

Yana magana ne akan wani mutum da hukumar EFCC ta kama a garin Ibadan, na jihar Oyo, da katin layikan waya wato SIM guda 116, ya yin da lamarin ya faru.

Kazalika lokacin faruwar lamarin, Bawa ya tsagaita da maganar mutumin inda ya rufe fuskarsa da tafin hannunsa na dama, yana mai cewa, “Don Allah, ku yi hakuri, ba zan iya ci gaba ba.” Inji shi.

Ministan Sadarwa da Bunkasa Tattalin Arzikin kasa, Dakta Isa Ali Pantami da wasu manyan jami’an Gwamnati ne, suka taimaka masa wurin zaunar dashi akan Kujera, sai dai Shugaban hukumar na EFCC ya fadi a kan kujerarsa nan take, ya yin da nan da nan aka fitar da shi.

Sai dai daga bisani Mai gabatar wa a wurin taron wato MC ya ba da sanarwar cewa, yanayin da Bawa ya shiga, ya dai-daita.

“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa Shugaban EFCC a yanzu ya samu natsuwa,” in ji shi.

Majiyar jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, har kawo hada wannan rahoton, wadanda suka hanzarta fitar da Shugaban na EFCC, har yanzu ba su koma cikin zauren da ake gudanar da Taron ba.

-Dimokuradiyya

No comments