Daga Muhammad A. Dalhatu Madogara ta labarto cewa; shugaban kasar Iran, Ebrahim Raeisi ya ce dole ne a hukunta Amurka bisa take hakkin Bil...
Daga Muhammad A. Dalhatu
Madogara ta labarto cewa; shugaban
kasar Iran, Ebrahim Raeisi ya ce dole ne a hukunta Amurka bisa take hakkin Bil’adama
da ta yi a yakin da ta kaddamar a Afghanistan, wanda suka kashe dubban mata da
kananan yara a yayin mamayar da suka yi.
Raesi
ya bayyana hakan ne a yayin zaman da ya yi da majalisarsa, inda ya kara da
cewa; abin da Amurka ta yi na tsawon shekaru 20 a Afghanistan ya nuna yadda ta
gwanance a take hakkin Bil’adama da take ‘yancinsu, inda suka rika kashe mata
da kananan yara tare da raunata wasu a yayin mamayarsu.
“idan muka dauki adadin mata da kananan yaran
da aka kashe, cin zarafinsu, da kuma raunata su a Afghanistan a tsawon shekaru
20, za mu ga irin mummunan bala’in da ya faru a kasar”, ya jaddada.
Ya
ce yakin da aka yi a Afghanistan yana tabbatar da cewa kasancewar sojojin
Amurka a sassa daban -daban na duniya bai taba ba da gudummawa wajen kawo tsaro
ba, sai dai ya lalata zaman lafiya, kwanciyar hankali da kuma tsaro.
No comments