Kungiyar Miyetti ta masu kiwon shanu ta Nijeriya (MACBAN) ta sanar da mutuwar Alhaji Abubakar Abdullahi, wanda aka fi sani da Danbardi, ...
Kungiyar Miyetti ta masu kiwon shanu ta Nijeriya (MACBAN) ta sanar
da mutuwar Alhaji Abubakar Abdullahi, wanda aka fi sani da Danbardi, Shugaban
Kungiyar a Karamar Hukumar Lere ta Jihar Kaduna.
Kungiyar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da Sakataren ta
na kasa, Othman Ngelzarma, ya bai wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya
(NAN) a ranar Asabar, a Abuja, yana mai cewa masu garkuwa da mutane sun kashe Marigayin,
mai shekaru 58 a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce "Mutuwar Abubakar ta kawo adadin jami'an MACBAN
biyar da 'yan bindiga, masu garkuwa da mutane ko barayin shanu suka kashe a
wannan shekarar a fadin kasar".
Ngelzarma ya bayyana cewa an tsinci gawar Abdullahi a bakin hanya a
ranar Juma’a, bayan an sace shi daga gidansa dake Lere a ranar 16 ga Satumba
kuma bayan an biya kudin fansa.
“An yi garkuwa da Alhaji Abubakar, mai shekaru 58 a ranar 16 ga
Satumba kuma bayan ya biya kudin fansa aka tsinci gawarsa a bakin hanya a ranar
Juma’a, 17 ga Satumba a wajen garin Lere.
"Yayin da muke jajantawa iyalan mamacin, MACBAN reshen jihar
Kaduna, muna kira ga hukumomin tsaro da su binciki wannan da sauran miyagun
ayyuka da dama a fadin kasar tare da gurfanar da masu laifin a gaban kuliya,"
in ji Ngelzarma.
Sakataren MACBAN na kasa ya yi tir da karuwar rashin tsaro da
membobin kungiyar ke fuskanta a duk fadin kasar, ko dai daga masu garkuwa da
mutane ko ‘yan bindiga.
Ya ce: “Kalubalen yana sa ku san ba zai yiwu membobinmu su gudanar
da harkokinsu cikin kwanciyar hankali ba. Wannan wani bangare ne da ke sanya tsadar
dabbobin da kayayyakin dabbobin.
“Idan rashin tsaron ya ci gaba, yana iya durkusar da harkar kiwon
dabbobi a kasar nan.
"Don haka muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta tabbatar da
cewa an aiwatar da sabbin manufofin da aka tsara domin inganta harkar
kiwo", in ji shi.
No comments