Daga Muhammad Haruna Manjo CL Datong, wanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi bayan da suka kai hari makarantar horas da sojoji ta ND...
Daga Muhammad Haruna
Manjo CL Datong, wanda ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shi bayan da
suka kai hari makarantar horas da sojoji ta NDA dake Kaduna a watan da ya
gataba, ya samu ‘yanci a karshe.
A yayin harin na ‘yan bindiga a ranar 24 ga watan Agustan 2021, an
kashe jami’an soji biyu.
A daren Juma’a ne, mataimakin Daraktan Hulda da jama’a na soji na
Division 1, Kanal Ezindu Idimah, shi ne ya bayyana cewa rundunarsu ce ta yi
nasarar ‘yanto Datong.
Ya ce samamen da suka kai wajen ‘yanto sojan ya sanya sun tarwatsa
sansanonin ‘yan bindiga da dama a Afaka zuwa Birnin Gwari dake jihar.
Ya ce sun kashe ‘yan bindiga da dama a yayin samamen, musamman
samamen da suka kai a daren ranar 17 ga watan Satumban 2021.
Ya ci gaba da cewa rundujar sojin tare da hadin guiwar sojin sama,
hukumar tsaro ta DSS, da sauran hukumomin tsaro, sun kai samamen ne cikin
hanzari inda suka gudanar a kafatanin yankin Afaka domin ‘yanto jami’in sojan
bayan da shugaban Hafsan sojojin Nijeriya ya bada umurni.
Sojojin sun isa sansanin da ake zargi shi ne wurin da ake tsare da
Manjo CL Datong. A sansanin, sojojin sun yi musayar wuta tare da 'yan bindigar inda
suka sha karfinsu.
“A cikin haka, sojojin sun galabar
nasarar kubutar da jami’in da aka sace. Duk da haka, jami’in ya samu rauni
kadan amma an yi masa magani a wani asibiti kuma an mika shi ga NDA don ci gaba
da daukar mataki, ”inji shi.
Ya yaba da kokarin NAF, DSS, 'Yan sandan Nijeriya da "yan
Najeriya masu kishin kasa" saboda tallafin da aka su wanda ya ce taimaka
wajen nasarar aikin da suka yi.
Ya ce su za su ci gaba har sai sun kamo ko kuma sun kashe maharan
da suka kashe jami’ai biyu (2) a cikin NDA.
No comments