Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Sojoji Nijeriya 'Sun Kashe 'Yan Fashin Daji Sama Da Hamsin A Kaduna'

  Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin saman Nijeriya na samun nasara a hare-hare ta sama da take kai wa sansanonin 'yan fashin daji d...

 


Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin saman Nijeriya na samun nasara a hare-hare ta sama da take kai wa sansanonin 'yan fashin daji da ke jihar Zamfara da kuma Kaduna.

Kafar watsa labarai ta PRNigeria ta ruwaito cewa jiragen saman sojojin kasar sun kai hari a sansonin yan fashin dajin da ke dajin Kawara a karamar hukumar Igabi da ke jihar Kaduna.

Wata majiyar tsaro ta ce 'yan fashin daji kusan hamsi ne suka hallaka a hare-haren ta sama a karshen mako

Majiyar ta kuma ce wani jirgin sama mai saukar ungulu na rundunar sojin sama ya gano wani gungun yan fashin daji sanye da bakaken tufafi, tare da shanu da suka sace kusa da kauyen Kawara a karamar hukumar Giwa.

"Lokacin da suka hango jirgin saman, yan bindigar sun tsere sun buya tsakanin shanu", in ji majiyar.

Majiyar ta kuma ce bayan da yan bindigar suka taru a wani wurin tsallaka ruwa, jirgin saman ya rika yi musu luguden wuta.

"Wasu daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sun rika kokarin tserewa lokacin da jirgin saman ya yi mu su luguden wuta", a cewar PRNigeria.

BBC ba ta samu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da hakan ba.

Sai dai wasu majiyoyi sun ce an kirga gawawwakin yan fashin daji akalla 50 a kauyen Kawara a ranar Litinin, yayin da aka lalata musu baburansu da abincinsu da ke sansanoninsu a hari ta sama.

Mahukuntan Najeriya sun kara kaimi a kwanakin baya baya nan a matakan da suke dauka domin magance matsalar yan fashin daji.

Baya ga hare-hare ta sama, mahukunta a Najeriya sun kuma dauki matakan dakatar da layukan sadarwa a jihar ta Zamfara.

Sai dai masana sun ce idan ana son matakin ya yi, akwai bukatar ganin cewa mahukuntan Najeriyar sun hada karfi da karfe da kasashe makwabta.


No comments