Rahotanni daga jihar Borno, na cewa, dakarun kasar sun kai hari maboyar mayakan ISWAP a karamar hukumar Kukawa, inda suka yi nasarar kashe...
Rahotanni daga jihar Borno, na cewa, dakarun kasar sun kai hari maboyar mayakan ISWAP a karamar hukumar Kukawa, inda suka yi nasarar kashe ‘yan kungiyar, da masu taimaka musu 28.
Sakamakon harin da sojoji suka kai ranar Lahadin da ta gabata, a sansanin ‘yan ta’addan yankin Kudancin Afrika ISWAP, akalla ‘yan kingiyar da masu mara musu baya na cikin masu sana’ar kamun kifi 28 ne suka gamu da ajalin.
Sojojin da ke yankin arewa maso gabashin Nijeriyar, a jihar Borno sun ce, mayakan ISWAP din da masu taimaka musu ne aka kashe a harin da sojojin suka kai a Daban Masara dake karamar hukumar Kukawa.
A cewar mai Magana da yawun sojojin, yankin na karkashin ikon mayakan ISWAP ne, inda suke haduwa da wadanda ke taimaka musu da wasu kayayyaki irin su, makamai da man fetur da kayan abinci da kuma ababan hawa.
Kakakin sojan, ya ce, sun haramtawa kowa zama a yankin, don ayyukan kamun kifi, saboda haka, duk wanda ke zama a yankin dan ta’adda ne.
No comments