Kungiyar Taliban ta sanar da kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Afghanistan, wata guda bayan kwace iko da kasar daidai lokacin dandazon...
Kungiyar
Taliban ta sanar da kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Afghanistan, wata guda
bayan kwace iko da kasar daidai lokacin dandazon matan ke ci gaba da
zanga-zangar neman ‘yanci da kuma shigar da su harkokin tafiyar da gwamnati.
A
wani taron manema labarai da kakakin kungiyar Zabihullah Mujahid ya gabatar a yau
Talata, ya sanar da cewa dukkanin mukaman da za a nada yanzu za su kasance na
rikon kwarya inda ya bayyana Mullah Mohammad Hasan Akhund a matsayin shugaban
sabuwar gwamnatin yayin da guda cikin ma’assasan kungiyar ta Taliban Abdul
Ghani Baradar zai zama mataimaki.
Haka
zalika Mujahid ya sanar da sunan Mullah Yaqub, dan Marigayi Mullah Omar tsohon
shugaban majalisar koli kuma guda cikin wadanda suka kafa kungiyar a matsayin
ministan tsaro sai kuma Sirajuddin Haqqani a matsayin ministan cikin gida wanda
shi ne tsohon mataimakin shugaban kungiyar ta Taliban.
Haka
zalika nade-naden na Taliban ya sanar da sunan Amir Khan Muttaqi babban mai
shiga Tsakani na kungiyar a Doha matsayin ministan harkokin waje.
A
cewar Mujahid Taliban za ta yi kokarin shigar da wasu mutane daga waje cikin
kowanne sashe na kasar don ba su mabanbantan mukamai.
No comments