Tsohon ministan Sufurin jiragen sama, Cif Femi Fani-Kayode (FFK) ya sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar A...
Tsohon ministan Sufurin jiragen sama, Cif Femi Fani-Kayode (FFK) ya sauya sheka daga jam'iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC da ke mulkin Nijeriya.
An gabatar da Fani-Kayode ga shugaba kasa Muhammadu Buhari a fadar Aso Villa da ke Abuja a karkashin jagorancin shugaban riko na jam’iyyar APC gwamnan Yobe, Mai Mala Buni a yau Alhamis.
Gwamnan Zamfara Bello Matawalle na cikin wadanda suka karbi Fani-Kayode a fadar gwamnatin. Fani-Kayode ya shaida cewa akwai dalilai da suka tilasta masa sauya sheka daga PDP zuwa APC, kuma ciki akwai neman hada-kan kasa.
Kayode ya shahara a baya da caccakar manufofin gwamnatin shugaba Buhari, musamman a shafukan sada zumunta, an kwana biyu dama ana rade-radin tsohon Ministan zai koma Jam’iyyar APC, amma sai yau lamarin ya tabbata kamar yadda majiyarmu ta Jaridar LEADERSHIP ta labarto.
No comments