Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tsohon Shugaban Kasar Algeria Bouteflika Ya Rasu Yana Da Shekaru 84

  Rfi ta labarto cewa tsohon shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya rasu da maraicen Juma’a yana da shekaru 84, kamar yadda fadar s...

 


Rfi ta labarto cewa tsohon shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya rasu da maraicen Juma’a yana da shekaru 84, kamar yadda fadar shugaban kasar ta sanar, sama da shekaru biyu bayan sauka daga mukaminsa sakamakon matsin lamba daga masu zanga-zanga da sojojin kasar.

Bouteflika, gogaggen dan gwagwarmayar neman 'yancin kai na Aljeriya, ya shafe shekaru ashirin yana mulkin kasar da ke Arewacin Afirka kafin ya yi murabus a watan Afrilun shekarar 2019 bayan gagarumin zanga -zangar watsi da shirinsa na neman wa'adi na biyar.

Ba kasafai aka gan tsohon shugaban ba a bainar jama'a ba tun a shekarar 2013 lokacin da ya gamu da mutuwar bangaren jiki.

Bayan murabus din Bouteflika, a wani yunkuri na kawo karshen zanga -zangar neman juyin juya halin siyasa da tattalin arziki, hukumomi sun kaddamar da binciken da ba a saba gani ba kan cin hanci da rashawa, wanda ya kai ga daure wasu manyan jami'ai da dama, ciki har da babban dan uwan ​​Bouteflika kuma mai ba sa shawara, Said.

Bayan samun 'yancin kan Aljeriya daga Faransa a shekarar 1962, tsohon shugaban kasa Bouteflika ya zama ministan harkokin waje na Aljeriya na farko kuma mai fada a ji a kasar.

No comments