Tawagar ‘yan wasan Young Boys ta kasar Switzerland ta shammaci Manchester United ta kasar Ingila da ci 2-1 a gasar cin kofin zakarun nahiy...
Tawagar ‘yan wasan Young Boys ta kasar
Switzerland ta shammaci Manchester United ta kasar Ingila da ci 2-1 a gasar cin
kofin zakarun nahiyar turai ta UEFA.
Dan wasan Young Boys Siebatcheu ne ya ceto
kungiyarsa gab da ana shirin kammala wasan bayan karin lokaci da aka yi.
Gabanin kwallon ta Siebatcheu, wasan yana ci
1-1.
Cristiano Ronaldo ne ya fara ci wa United
kwallo a minti na 13 a wannan wasa nata da ya kasance na farko a sabuwar kakar
wasa ta Champions League.
Sai dai ana shirin tafiya hutun rabin lokaci
alkalin wasa ya ba Wan- Bissaka jan kati bayan da ya same shi da laifin yin
shigar mugunta ga dan wasan Young Boys Martins.
Hakan ya sa Manchester United ta karasa wasan
da ‘yan kwallo 10, abin da Young Boys ta yi amfani da shi ta farke kwallon.
Dan wasan Young Boys Ngamaleu ne ya farke
kwallon farko a minti na 66.
Ole Gunner Solskjaer ya cire Ronaldo a wasan,
ya maye gurbinsa da Jesse Lingard, wani abu da masu fashin baki suka ce dabara
ce ta kare lafiyar fitaccen dan wasan.
Ko da yake, wasu na ganin sauyin ya taimaka
wajen kayen da United ta sha a hannun Young Boys.
No comments