Waɗanda Suka Yi Yunkurin Murkushe Mu Ba Su Yi Nasara Ba, A Cewar Shaikh ZakzakyDaga Wakilinmu a Abuja

Jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Shaikh Ibraheem Zakzaky, a makonnnin da suka gabata, ya bayyana cewa, waɗanda ke neman rusa su bayan kisan kiyashin Zariya dda ya gudana a shekarar 2015 ba su samu nasara ba.

Jaridar Blueprint Manhaja ta labarto cewa; Shaikh Zakzaky ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa ta tafiyar ta su a Abuja.

Ya yi bayanin cewa zaluncin da aka yi wa Harkar Musulunci a Nijeriya, wanda ya cika shekaru shida na zaman gidan yari ya kara fantsama al'amarin Harkar Musulunci a dukkannin faɗin duniya.

Shaikh Zakzaky ya ce, “yayin da aka ƙaddamar da farmakin gaba ɗaya da nufin murƙushe Harkar Musulunci, ba a yi nasara da wani abu ba face ɗaukaka Harkar zuwa matakin da ba a yi tsammani ba.”

“Za mu iya cewa kisan gillar da aka yi a Zariya a shekarar 2015 wani lokaci ne na gwaji wanda ya shafi jama’a.”

Ya yaba wa dukkan ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam na cikin gida da na waje da ƙungiyoyin jin ƙai da ke ci gaba da matsa lamba don a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba daga tsare shi tare da biyan buƙatun mabiyansa, waɗanda suka sami raunuka da asara daban-daban a ƙoƙarin neman ‘yancinsa.

Jagoran na Harkar Musulunci ya jajantawa iyalan da suka rasa ‘yan'uwansu yayin harin sojoji na 2015 a kan Harkar da kuma neman adalci.

Ya yi addu’ar Allah ya saka musu da alkhairi ya kuma sa aljanna ce makomarsu ta ƙarshe.

Post a Comment

0 Comments