Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Wata Kungiya A Katsina Ta Sha Alwashin Horar Da Mata Sana’o’in Hannu

Daga Abdulrazak Ahmad Jibia Cibiyar "Fire Works" wacce Kungiyar "Jibia Peoples Forum" ta kirkira a watan Fab...Daga Abdulrazak Ahmad Jibia

Cibiyar "Fire Works" wacce Kungiyar "Jibia Peoples Forum" ta kirkira a watan Fabrairun 2021, ta dukufa wajen koyawa 'yan mata da matan aure sana'o'in hannu domin su yi dogaro da kansu.

A karon farko, ranar 1 ga watan Afrilun 2021 dalibai 34 ne suka yi rijista, suka yi karatu na tsawon watanni 3, suka kuma koyi yadda ake kera sarka, 'yan kunne, 'yan hannu, da zobe; kuma aka yaye su ranar 12 ga watan Yuni.

Kazalika, ranar 5 ga Satumban shekarar, dalibai 50 ne suka yi rijista; wadanda za a yaye su bayan makonni 12 masu zuwa.

Kamar yadda ya shaidawa wakilinmu, Babban Sakataren kungiyar Malam Bishir Crazy, ya bayyana cewa "kungiyar Jibia Peoples Forum ce ta dauki nauyin wannan aiki, amma kuma a lokacin da muka yi bikin yaye dalibai a karo na farko mun samu goyon baya da gudunmuwar Honorabul Aminu Lawal (Dan Malikin Jibia) mai bada shawara na musamman akan Sana'o'in hannu ga mai girma gwamnan Jihar Katsina Honorabul Aminu Bello Masari."

A na ta jawabi shugabar makarantar kuma Malamar dake koyarwa dalibai Sana'o'in, Aisha Muhammad, ta tabbatar da cewa suna yin duk mai yiwuwa wajen koyawa daliban abin da ya kamata har sai sun fahimta.

Ta kara da cewa "Tsarin koyarwar biyu ne, a rubuce da kuma a aikace". 

A yayin da suke jawabi, wasu daga cikin daliban makarantar, sun bayyana jin dadinsu bisa kokarin da kungiyar ke yi, tare da jinjina a bisa jajircewar da Malamansu ke yi. Sannan sun bayyana shirin a matsayin babbar nasara a gare su, kuma hanya ce da za ta sa su yi dogaro da kawunansu, su taimaki danginsu, da 'ya'yansu da mazajen aurensu.

Daga karshe shugaban kungiyar Alhaji Gidde Dahiru, ya yi kira ga gwamnatin jihar Katsina da ta taimaki wannan gidauniya wacce kungiyar Jibia Peoples Forum ta kawo domin ganin an taimaki al'umma ta fuskar koyar da su sana'o'in hannu wadanda za su magance zaman banza, tare da bada jari ga dukkanin daliban da suka kammala karatu domin su je su kafa cibiyar sana'ar da suka koya.

An gudanar da shirin ne a harabar makarantar Firamare ta Muhammadu Rabi'u garin Jibia a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
No comments