Daga Wakilinmu
A wani abu mai kama da Baraka ce ta shiga
tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da Lauyoyinsa wanda ta kai ga a zaman
shari’ar da aka yi a yau Alhamis suka sanar da kotu cewa sun janye wakiltarsa
da suke yi, wata sabuwa ta bullo bayan kammala shari’ar ta yau wacce aka dage
aka sanya ranar 30 ga watan Satumban nan domin ci gaba da shari’ar.
Barista Rabiu Shu'aibu Abdullahi
wanda yake jagorantar tawagar Lauyoyin Sheikh Abduljabbar a baya kafin su janye
ya ce sun bai wa Shehin Malamin mako biyu ya yi karar su a hukumance bisa zarge
zargen da ya yi musu a zaman kotu da aka yi yau, idan kuma ba haka ba za su
dauki matakin shari’a a kansa.
Jarida Radio ta labarto cewal
Barista Rabiu ya musanta dukkan zarge zargen da Sheikh Abdujabbar yayi musu a
kotu yau. Ya kuma shaida cewa ba za su bayyana mene ne ya sa suka janye daga shari'ar
ba, domin ya saɓa da dokar aikin su na Lauyoyi su bayyana abin da ya faru na saɓani
tsakanin su da wanda suke wakilta.
Ya kara da cewa akwai bangare na
musamman da Shari'a ta ware da wanda suke wakilta zai iya kai ƙarar Lauyoyinsa
bisa sauka daga tsarin aiki da suka yi.
A yau ne Sheikh Abduljabbar ya
bayyana wasu tuhume tuhume akan Lauyoyinsa a kotu bayan an tambaye shi kan
janyewarsu daga kare shi.
Sheikh Abduljabbar ya ce yana zargin
Lauyoyinsa sun cinye kudi da suka ce za su yi hira da ‘yan jarida domin ya
bayyana musu al'amura game da shari'ar da ta gabata a ranar 2 ga watan Satumba,
sannan kuma sune suka sa shi ya yi shiru a zaman da aka yi na baya lokacin da Alƙali
ya tambaye shi game da sababbin tuhumomin da ake yi masa.
0 Comments