Rahotannin da MADOGARA ta samu na nuni da cewa; Jami'an Hukumar Kwastam ta Nijeriya sun budewa Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin ...
Rahotannin da
MADOGARA ta samu na nuni da cewa; Jami'an Hukumar Kwastam ta Nijeriya sun budewa Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu ta jihar Katsina, Alhaji Ya'u Umar Gwajo Gwajo wuta a hanyarsa ta Daura zuwa Katsina.
Lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata a daidai garin Mai Aduwa daga Daura.
Ya zuwa yanzu babu labarin raunata wa daga tawagar Kwamishinan ko rasa rai.
 |
Yadda harsashi ya fasa motar. |
 |
Jami'an Kwastam din na kokarin dakile daukarsu hoto. |
 |
Motar Jami'an Kwastam din. |
 |
Yadda harsashi ya fasa bayan motar Hilux na tawagar Kwamishinan. |
No comments