Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Lauyoyina Suka Yaudare Ni Da Zambata Ta -Shaikh Abduljabbar

Daga Wakilinmu Malamin Addinin Musuluncin nan a nan Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana abin da ya hada shi da lauyoyinsa har ...


Daga Wakilinmu

Malamin Addinin Musuluncin nan a nan Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana abin da ya hada shi da lauyoyinsa har suka juya masa baya kamar yadda Kano Focus ta labarto.

Malam Kabara ya ce lauyoyinsa sun bukaci ya ba su naira miliyan daya da rabi (N 1, 500, 000) domin su shirya taron manema labarai.

Malamin ya bayyana hakan ne lokacin da yake yi wa kotu bayani, a wani bagare na ci gaba da shari’ar da ake yi masa a jiya Alhamis.

Ya ce sun nemi kudin ne da zummar su yi taron manema labarai su nuna yadda aka zalunce shi ko jama’a sa tausaya masa.

Ya kara da cewa kwanaki biyu kafin a yi zaman kotun baya lauyoyinsa sun same shi a gidan kurkuku, suka ce masa za a koma kotu za kuma a ci gaba tuhumarsa.

“Sun same ni a gidan yari na Kurmawa, inda nake tsare, suka ce min dukkan tuhumar da ake yi min gadar zare ce kawai.

“Sun ce idan na amince da tuhumar to ba shakka na fada cikin tarkon da aka dana min.

“Suka kuma gayan tuni aka yanke min hukunci jira ake kawai na amsa a zartar da shi.” A cewarsa.

Na zama kurma

Sheikh Abduljabbar Kabara ya kara da cewa lauyoyin sun bukaci da ya kame bakinsa da zarar anje kotun kada ya ce uffan.

Ya ce sai dai ya tambaye su mai zai biyo baya idan ya kulle bakinsa ya ce ba zai yi magana ba?

Inda ya ce sun gayamasa kar ya damu za su kula da al’amarin, shi dai kada ya yi magana.

Haka kuma ya ce sun nemi ya ba su naira dubu dari biyar (N500, 000) domin su shirya taron 'yan jaridar.

“Bayan sun gama wancan bayanin ne kuma suka bukaci na ba su dubu dari biyar su yi taron ‘yan jarida.

“Hakan ta sanya na ba su dubu dari uku (N300, 000), na kuma zo kotu na kame bakina kamar kurma”.

“Bayan na kame bakina ne kuma Alkali ya ce a yi min gwajin kwakwalwa da na kunne, amma lauyoyin nan suka kasa cewa komai”, ya kara da cewa.

Wani jami’in gwamnati zai taimakeni

Abduljabbar Kabara ya ci gaba da gayawa kotu cewa, lauyoyin nasa sun hada shi da wani babba a gwamnati don ya taimaka masa.

Ko da dai ya ce ba zai fadi sunansa ba, amma ya yi masa wasu bayanai.

Dole na yarda inda ciwon hauka

Malamin ya ce mutumin da aka hada shi da shi ya gaya masa idan aka tabbatar da shi mahaukaci ne to rayuwarsa za ta tagayyara.

Sai dai ya gaya masa zai kuma shaki iskar ‘yanci, amma zai ci gaba da rayuwarsa a matsayin mahaukaci.

Don haka ya ce sun nemi ya ba su milyan daya, don su kira taron manema labarai a karo na biyu su magance duk wani abu da zai bata masa suna.

“Sun nemi na ba su naira miliyan daya (N1, 000, 000) su yi taron manema labarai, don su kare min martaba ta da sunana.

“Amma sai suka ce dole idan za a yi haka sai na yarda ina da tabin kwakwalwa, sannan za su taimakamin a sake ni.

Za a kwace min mata

Haka zalika malamin ya ce lauyoyin sun yi yunkurin kwace masa mata.

A cewarsa bayan da aka bukaci a yi masa gwajin kwakwalwa lauyoyin sun yi kokarin kulla alaka da matarsa. Ya ce al’amarin bai yi masa dadi ba, inda ya ce hakan cin zarafi ne.

Zarge-zargen ba gaskiya bane

Sai dai lauyoyin na sa sun musunta dukkanin zarigin da malamin ya yi musu.

Barista Rabi’u Shu’aibu Abdullahi ne ya musanta zargi a wani bagare na mayar da martani ga kalaman na Sheikh Abduljabbar.

Ya ce idan Abduljabbar yana gani an yi masa ba daidai ba to akwai inda aka tsara ya kai karar lauyoyin.

Ya ce idan ya kai kara a nan ne lauya zai kare kansa kan duk wani zargi da aka yi masa, 

Ko ya shigar da kara ko mu bi hakkin mu

Haka zalika Barista Abdullahi ya ce sun bai wa malamin makwanni biyu ya shigar da karar neman hakkinsa kan zargin da yake yi musu.

Ya ce hukumar da aka tanada don kai karar lauya ba a boye mata dukkanin bayanai.

A don hakan nema ya ce sun bashi makwanni biyu ya kai karar ko kuma su su nemi na su hakkin.


-Kano Focus


No comments