Mafarautar gargajiya sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 47 da suka hana mutanen Shiroro dake Jihar Neja zaman lafiya na dogon lokaci. Jar...
Mafarautar
gargajiya sun yi nasarar kashe ‘yan bindiga 47 da suka hana mutanen Shiroro
dake Jihar Neja zaman lafiya na dogon lokaci.
Jaridar
PRNigeria da ake wallafawa a Nijeriya ta ce mafarautar sun kaddamar da harin ne
a Magami dake tsakanin kananan hukumomin Shiroro da Rafi inda suka hallaka ‘Yan
bindigar a ranar larabar da ta gabata.
Majiyar
jaridar tace ‘yan bindigar sun dade suna amfani da ‘yankin dake kusa da gabar
ruwa wajen fakewa suna kai wa jama’a hare hare a yankunan jihar.
Jaridar
ta ce wani jami’in ‘Yan sanda ya tabbatar mata cewar bayan kashe 47 daga cikin
su, wasu da dama sun tsere da harbin bindiga a jikin su.
Jihar
Neja na daya daga cikin jihohin da ‘Yan bindiga suka hana jama’a sakewa, inda
suke kai hari garuruwa suna kashe mutane da kuma kwashe wasu domin karbar kudin
fansa.
Rfi Hausa ta labarto cewa; ko a
makon jiya sanda ‘Yan bindigar suka karbi kudin fansa kafin sakin daliban
Islamiyar Tegina wadanda suka kwashe kwanaki 88 a hannun su.
Gwamnan
Jihar Abubakar Sani Bello ya kafa wata rundunar ‘Yan Sakai dake samun tallafin
sojoji da ‘Yan Sanda domin taimakawa jami’an tsaron tabbatar da zaman lafiya a
jihar.
Bello
ya ce ‘Yan bindigar sun jefa jama’ar sa cikin halin kakanikayi wajen hana
‘yayan su zuwa makaranta da hana jama’a tafiye tafiye da gudanar da harkokin
noma, amma kuma ba za su bada kai bori ya hau ba.
No comments